4 Sa'ad da shekara ta hamsin ta murnar Isra'ilawa ta kewayo, za a haɗa gādonsu da na kabilan mutanen da suka aura, da haka za a ɗebe gādonsu daga gādon kabilar kakanninmu.”
5 Musa kuwa ya umarci Isra'ilawa bisa ga faɗar Ubangiji ya ce, “Abin da mutanen kabilar 'ya'yan Yusufu suka faɗa daidai ne.
6 Abin da Ubangiji ya umarta a kan 'ya'ya mata na Zelofehad ke nan, ‘A bar su su auri wanda suka ga dama, amma sai a cikin iyalin kabilar kakansu.
7 Ba za a sāke gādon Isra'ilawa daga wata kabila zuwa wata ba, gama kowane mutum na cikin jama'ar Isra'ila zai riƙe gādonsa na kabilar kakanninsa.
8 Kowace 'ya mace wadda ta ci gādo a wata kabilar Isra'ila, sai ta yi aure a cikin kabilar kakanta domin kowane Ba'isra'ile ya ci gādon kakanninsa.
9 Ta yin haka ba za a sāke gādo daga wata kabila zuwa wata ba, gama kowace kabilar Isra'ila za ta riƙe gādonta.’ ”
10 Sai 'ya'yan Zelofehad mata, wato Mala, da Tirza, da Hogla, da Milka, da Nowa suka yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.