2 “Ka umarci Isra'ilawa su fitar da kuturu, da mai ɗiga, da wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, daga cikin zango.
3 Su fitar da mace ko namiji daga cikin zango, don kada su ƙazantar da zangonku inda nake zaune.”
4 Sai Isra'ilawa suka fitar da su daga cikin zango kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Haka mutanen Isra'ila suka yi.
5 Ubangiji kuma ya ba Musa
6 waɗannan ka'idodi domin Isra'ilawa. Idan wani ya aikata rashin gaskiya ga Ubangiji, ta wurin saɓa wa wani,
7 sai ya hurta zunubinsa, sa'an nan ya biya cikakkiyar diyyar abin da ƙarin humushin abin, ya ba mutumin da ya yi wa laifin.
8 Idan wanda ya yi wa laifin ya rasu, ba shi kuma da wani dangi na kusa wanda za a ba diyyar, sai a kai diyyar gaban Ubangiji domin firist, tare da ragon hadaya, don yin kafarar da za a yi masa.