8 Idan wanda ya yi wa laifin ya rasu, ba shi kuma da wani dangi na kusa wanda za a ba diyyar, sai a kai diyyar gaban Ubangiji domin firist, tare da ragon hadaya, don yin kafarar da za a yi masa.
9 Dukan sadakoki na tsarkakakkun abubuwa na Isra'ilawa waɗanda sukan kawo wa firist, za su zama nasa.
10 Kowane firist zai adana sadakokin da aka ba shi.
11 Ubangiji kuma ya umarci Musa
12-14 ya faɗa wa Isra'ilawa waɗannan ka'idodi. Idan mutum yana shayin matarsa kan tana yi masa rashin aminci, har ta ƙazantar da kanta ta wurin kwana da wani mutum, amma mijin bai tabbatar ba, domin ta yi abin a asirce, ba kuwa mai shaida, ba a kuma kama ta tana cikin yi ba, ko kuma mijin ya yi shayinta ko da ba ta aikata irin wannan laifi ba,
15 duk da haka sai mutum ya kawo matarsa a gaban firist, ya kawo kuma hadayar da ake bukata, wato humushin garwar garin sha'ir, amma kada ya zuba mai ko kayan ƙanshi, gama hadaya ce domin kishi, domin a bayyana gaskiya a fili.
16 Sai firist ya kawo ta kusa, ya tsai da ita a gaban Ubangiji.