3 sai ya keɓe kansa daga ruwan inabin da yake sa maye da ruwan inabi mai tsami. Kada kuma ya sha ruwan inabi mai tsami da yake sa maye da kowane irin abin sha da aka yi da 'ya'yan inabi mai tsami. Kada kuma ya ci ɗanyu ko busassun 'ya'yan inabi.
4 A dukan kwanakin nan da ya keɓe kansa, kada ya ci kowane irin abu da aka yi da kurangar inabi, ko da ƙwayar inabi ko da ɓawonsa.
5 A dukan kwanakin wa'adinsa na keɓewa, kada aska ta taɓa kansa, sai kwanakin keɓewar kansa ga Ubangiji sun cika. Zai zama mai tsarki, zai kuma bar sumarsa ta yi tsawo.
6 A dukan kwanakin da ya keɓe kansa ga Ubangiji, kada ya kusaci gawa.
7 Ko ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan'uwansa, ko ta 'yar'uwarsa, ba zai ƙazantar da kansa ba, tun da yake ya keɓe kansa ga Allahnsa.
8 Shi tsattsarka ne ga Ubangiji dukan kwanakin da ya keɓe kansa.
9 Idan farat ɗaya wani mutum ya rasu kusa da shi, to, keɓewarsa ta ƙazantu, sai ya aske kansa a ranar tsarkakewarsa a kan rana ta bakwai.