6 A dukan kwanakin da ya keɓe kansa ga Ubangiji, kada ya kusaci gawa.
7 Ko ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan'uwansa, ko ta 'yar'uwarsa, ba zai ƙazantar da kansa ba, tun da yake ya keɓe kansa ga Allahnsa.
8 Shi tsattsarka ne ga Ubangiji dukan kwanakin da ya keɓe kansa.
9 Idan farat ɗaya wani mutum ya rasu kusa da shi, to, keɓewarsa ta ƙazantu, sai ya aske kansa a ranar tsarkakewarsa a kan rana ta bakwai.
10 A rana ta takwas kuwa zai kawo wa firist 'yan kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu a bakin ƙofar alfarwa ta sujada.
11 Sai firist ya miƙa ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadayar ƙonawa, ya yi kafara dominsa, gama ya yi zunubi saboda gawa. A wannan rana zai sāke keɓe kansa.
12 Sai ya sāke keɓe kansa ga Ubangiji daidai da kwanakin da ya ɗauka a dā. Zai kawo ɗan rago bana ɗaya na yin hadaya don laifi. Kwanakin da ya yi a dā ba su cikin lissafi domin keɓewarsa ta dā ta ƙazantu.