19 Daga cikin Isra'ilawa kuwa na ba da Lawiyawa ga Haruna da 'ya'yansa maza don su yi wa Isra'ilawa hidima a alfarwa ta sujada, su kuma yi kafara dominsu don kada annoba ta sami Isra'ilawa sa'ad da suka kusaci alfarwa ta sujada.”
20 Musa da Haruna kuwa da dukan taron Isra'ilawa suka yi wa Lawiyawa yadda Ubangiji ya umarce Musa, haka kuwa Isra'ilawa suka yi musu.
21 Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka wanke tufafinsu. Haruna kuwa ya keɓe su, suka zama kamar hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji, ya kuma yi kafara dominsu don ya tsarkake su.
22 Bayan haka Lawiyawa suka shiga alfarwa ta sujada don su yi aiki a gaban Haruna da 'ya'yansa maza, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa a kan Lawiyawa, haka kuwa suka yi musu.
23 Ubangiji ya kuma ce wa Musa,
24 “Wannan ita ce ka'idar aikin Lawiyawa, tun daga mai shekara ashirin da biyar zuwa gaba, zai shiga yin aiki a alfarwa ta sujada.
25 Amma daga shekara hamsin, sai su huta daga aiki alfarwa ta sujada.