6 “Keɓe Lawiyawa daga cikin Isra'ilawa ka tsarkake su.
7 Ga yadda za ka tsarkake su. Ka yayyafa musu ruwan tsarkakewa. Su aske jikunansu duka, su kuma a wanke tufafinsu, sa'an nan za su tsarkaka.
8 Su kuma ɗauki maraƙi tare da lallausan garin hadaya kwaɓaɓɓe da mai. Kai kuma ka ɗauki wani maraƙi na yin hadaya don zunubi.
9 Sa'an nan ka gabatar da Lawiyawa a gaban alfarwa ta sujada, ka kira taron Isra'ilawa duka.
10 Sa'ad da ka gabatar da Lawiyawa a gaban Ubangiji, sai Isra'ilawa su ɗibiya hannuwansu bisa Lawiyawa.
11 Haruna kuma zai gabatar da Lawiyawan a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa daga Isra'ilawa domin su zama masu yi wa Ubangiji aiki.
12 Sa'an nan Lawiyawa za su ɗibiya hannuwansu a bisa kawunan maruƙan. Za ka yi hadaya domin zunubi da maraƙi ɗaya, ɗaya kuma ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji domin ka yi kafara saboda Lawiyawa.