19 Ko da girgije ya daɗe a bisa alfarwar Isra'ilawa ba sukan tashi ba, sukan bi umarnin Ubangiji.
20 Wani lokaci girgijen yakan yi 'yan kwanaki ne kawai bisa alfarwar. Tashinsu da zamansu sun danganta ga umarnin Ubangiji.
21 Wani lokaci girgijen yakan zauna a bisa alfarwar daga maraice zuwa safiya ne kawai, sa'an nan ya tashi, su kuma sai su tashi. Amma idan girgijen ya yini, ya kwana, sa'an nan ya tashi, su kuma sai su tashi.
22 Ko kwana biyu ne girgijen ya yi, yana zaune a bisa alfarwar ko wata guda, ko fi, sai Isra'ilawa su yi ta zamansu a zangon, ba za su tashi ba. Amma in ya tashi, sai su kuma su tashi.
23 Da umarnin Ubangiji suke sauka, da umarninsa kuma suke tashi, suna bin faɗarsa, yadda ya umarci Musa.