26 Shekara ɗari uku Isra'ilawa suka yi zamansu a Heshbon da ƙauyukanta, da Arower da ƙauyukanta, da dukan biranen da suke a gefen Kogin Arnon, me ya sa ba ka ƙwace su tun a wancan lokaci ba?
27 Don haka ni ban yi maka laifi ba, kai ne kake yi mini laifi da kake yaƙi da ni. Ubangiji ne alƙali yau, zai shara'anta tsakanin Isra'ilawa da Ammonawa.”
28 Amma Sarkin Ammonawa bai kula da saƙon da Yefta ya aika masa ba.
29 Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko wa Yefta, sai ya tashi ratsa Gileyad da Manassa zuwa Mizfa ta Gileyad, daga can ya haura zuwa wurin Ammonawa.
30 Yefta kuwa ya yi wa'adi ga Ubangiji, ya ce, “Idan dai ka ba da Ammonawa a hannuna,
31 duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don ya tarye ni, sa'ad da na komo daga yaƙin Ammonawa da nasara, zai zama na Ubangiji, zan kuwa miƙa shi hadaya ta ƙonawa.”
32 Yefta ya haye zuwa wurin Ammonawa domin ya yi yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannunsa.