15 Ya kuwa sami sabon muƙamuƙin jaki, ya ɗauka ya kashe mutum dubu da muƙamuƙin.
16 Sa'an nan Samson ya raira waƙa ya ce.“Da muƙamuƙin jaki na kashe mutum dubu,Da muƙamuƙin jaki na tsiba su tsibi-tsibi.”
17 Da ya gama, ya jefar da muƙamuƙin. Sai aka ba wurin suna, Ramat-Lihai, wato tudun muƙamuƙi.
18 Ƙishirwa kuwa ta kama shi ƙwarai, sai ya roƙi Ubangiji ya ce, “Kai ne ka yi wannan babbar nasara ta hannun bawanka, yanzu kuwa ko zan mutu da ƙishirwa, har Filistiyawa marasa kaciya su kama ni?”
19 Allah kuwa ya buɗe wani rami daga ƙasa, sai ruwa ya ɓuɓɓugo daga ciki. Da ya sha, hankalinsa ya komo, ya wartsake. Don haka aka ba wurin suna En-hakkore, wato mai kira. Ramin yana nan a Lihai har wa yau.
20 Samson ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin a zamanin da Filistiyawa suke mulkinsu.