19 Suka ce masa, “Yi mana shiru, kame bakinka. Ka biyo mu, ka zama firist namu da mai ba mu shawara. Bai fi kyau ka zama firist na kabilar Isra'ila ba, da a ce ka zama na gidan mutum guda kawai?”
20 Da firist ɗin ya ji haka, sai ya yi murna, ya ɗauki falmaran da kan gida da sassaƙaƙƙen gunki, ya tafi tare da su.
21 Suka juya, suka tafi da 'ya'yansu da dabbobinsu, da mallakarsu.
22 Sa'ad da suka yi 'yar tazara daga gidan Mika sai aka kira maƙwabtan Mika, suka je suka ci wa Danawa.
23 Suka yi wa Danawa tsawa. Da suka waiga, sai suka ce wa Mika, “Me ya faru? Me ya kawo waɗannan 'yan iska?”
24 Mika kuwa ya ce musu, “Kun kwashe allolina da na yi, da firist ɗina, me ya rage mini kuma? Sa'an nan ku ce mini, ‘Me ya faru?’ ”
25 Danawa kuma suka ce masa, “Kada ka kuskura ka ce kome, idan ba haka ba mutanen nan za su harzuƙa, da kai da iyalinka duka ku rasa rayukanku.”