1 A lokacin nan ba sarki a Isra'ila. Sai wani Balawen da yake zama a wani lungu na ƙasar tudu ta Ifraimu ya ɗauko wata mace daga Baitalami ta Yahudiya ta zama ƙwarƙwararsa.
2 Ƙwarƙwarar kuwa ta ji haushinsa, ta koma gidan mahaifinta a Baitalami ta Yahudiya. Ta zauna a can har wata huɗu.
3 Sa'an nan mutumin ya tafi ya yi bikonta. Ya tafi da baransa da jaki biyu. Da ya zo gidan mahaifinta, sai ta shigo da shi gidan, mahaifin ya karɓe shi da farin ciki.
4 Mahaifin macen ya i masa ya dakata, sai ya tsaya har kwana uku. Suka ci suka sha tare.
5 A safiyar rana ta huɗun, suka tashi tun da wuri, domin su yi shirin tafiya, amma mahaifin matar ya ce masa, “Ka dakata ka ƙara cin abinci tukuna sa'an nan ka tafi.”
6 Su biyu kuwa suka zauna suka ci suka sha tare. Har yanzu mahaifin mace ya sāke ce masa, “Ina roƙonka ka ƙara kwana, ka saki jikinka ka more.”