8 A rana ta biyar, sai mutumin ya tashi da wuri don ya tafi amma mahaifin macen ya ce masa, “Ka zauna ka ci abinci tukuna har rana ta yi sanyi.” Dukansu biyu suka zauna suka ci tare.
9 Sa'ad da mutumin, da ƙwarƙwararsa, da baransa sun tashi za su tafi, sai mahaifin macen kuma ya ce masa, “Ga shi, rana ta kusan faɗuwa, yamma kuwa ta yi, ina roƙonka, ka sāke kwana ka ji wa ranka da:di, sa'an nan ka yi sammako gobe ka kama hanyarka zuwa gida.”
10 Amma mutumin bai yarda ya sāke kwana ba, sai ya tashi shi da ƙwarƙwararsa suka kama hanya. Ya kai daura da Yebus, wato Urushalima ke nan. Yana tare da jakinsa biyu da ya yi musu shimfiɗa, da ƙwarƙwararsa.
11 Baran kuwa ya ce wa maigidansa, “In ka yarda mu ratse mu kwana a birnin Yebusiyawan nan.”
12 Amma maigidansa ya ce masa, “Ba za mu tsaya a birnin da mutane ba Isra'ilawa ba ne. Za mu wuce zuwa Gibeya,
13 mu ƙara ɗan nisa, mu tafi mu kwana a Gibeya ko a Rama.”
14 Sai suka wuce, suka yi tafiyarsu. Rana ta faɗi sa'ad da suka kai Gibeya, ta yankin ƙasar Biliyaminu.