1 Dukan jama'ar Isra'ila fa suka fito tun daga Dan a arewa har zuwa Biyer-sheba a kudu da kuma Gileyad daga gabas. Suka hallara gaba ɗaya a gaban Ubangiji a Mizfa.
2 Dukan shugabannin kabilar Isra'ila suna cikin wannan taron jama'ar Allah. Sojojin ƙafa yawansu ya kai dubu ɗari huɗu (400,000).
3 Mutanen Biliyaminu kuwa sun ji labari sauran Isra'ilawa sun haura zuwa Mizfa. Isra'ilawa suka tambayi Balawen suka ce, “Ka faɗa mana yadda wannan mugun abu ya auku.”
4 Balawe, mai ƙwarƙwarar da ka kashe, ya amsa ya ce, “Ni da ƙwarƙwarata muna biyo Gibeya ta Biliyaminu mu kwana.