18 Isra'ilawa suka tashi suka tafi Betel. A can suka yi tambaya ga Allah suka ce, “Wace kabila ce daga cikinmu za ta fara faɗa wa kabilar Biliyaminu?”Ubangiji ya ce, “Kabilar Yahuza ce za ta fara.”
19 Sa'an nan Isra'ilawa suka tashi da safe suka kafa sansani kusa da Gibeya.
20 Suka kuwa fita su yi yaƙi da mutanen Biliyaminu, suka jā dāgar yaƙi suna fuskantar Gibeya.
21 Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu ashirin da biyu (22,000), daga cikin mutanen Isra'ila a ranar.
22-23 Mutanen Isra'ila suka tafi inda ake sujada suka yi makoki a gaban Ubangiji har zuwa dare. Suka tambaye shi suka ce, “Mu sāke zuwa domin mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu mutanen Biliyaminu?”Ubangiji ya ce musu, “I, ku tafi.”Saboda haka sai sojojin Isra'ilawa suka ƙarfafa, suka sāke jān dāga a inda suka jā ta dā.
24 Sai mutanen Isra'ila suka tafi su kara da mutanen Biliyaminu a rana ta biyu.
25 Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu goma sha takwas (18,000) daga cikin Isra'ilawa. Dukan waɗannan da aka hallaka horarru ne.