1 “Ku 'ya'ya ne ga Ubangiji Allahnku, kada ku yi wa jikinku zāne, kada kuma ku yi wa kanku sanƙo saboda wani wanda ya rasu.
2 Gama ku keɓaɓɓun mutane ne na Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku kuwa ya zaɓo ku daga cikin dukan al'umman duniya ku zama mutanensa, wato abin gādonsa.”
3 “Kada ku ci abin da yake haram.
4 Ga dabbobin da za ku ci, da saniya, da tunkiya, da akuya,
5 da mariri, da barewa, da mariya, da mazo, da makwarna, da gada, da ɓauna, da ragon dutse.
6 Za ku iya cin kowace dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take tuƙa.
7 Amma duk da haka cikin waɗanda suke tuƙa, da waɗanda suke da rababben kofato ba za ku ci raƙumi, da zomo, da rema ba, ko da yake suna tuƙa, amma ba su da rababben kofato. Haram ne su a gare ku.