13 Sai ku zama marasa aibu a gaban Ubangiji Allahnku.
14 “Gama waɗannan al'ummai da za ku kora suna kasa kunne ga masu maita da masu duba, amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba.
15 “Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamata daga cikin jama'arku, sai ku saurare shi.
16 “Wannan shi ne abin da kuka roƙa a wurin Ubangiji Allahnku a Horeb, a ranar taron, gama kun ce, ‘Kada ka bar mu mu ƙara jin muryar Ubangiji Allahnmu, ko mu ƙara ganin wannan babbar wuta, don kada mu mutu,’
17 Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Abin da suka faɗa daidai ne.
18 Zan tayar musu da wani annabi kamarka daga cikin 'yan'uwansu. Zan sa magana a bakinsa, zai faɗa musu duk abin da na umarce shi.
19 Duk wanda bai saurari maganata wadda zai faɗa da sunana ba, ni da kaina zan nemi hakkinta a gare shi.