1 Musa da dattawan Isra'ila suka umarci jama'a, suka ce, “Ku kiyaye dukan umarnai waɗanda na umarce ku da su yau.
2 Bayan da kuka haye Urdun, kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku kakkafa manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa.
3 Sai ku rubuta kalmomin wannan shari'a a kansu daidai lokacin da kuka haye ku shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta wa kakanninku.
4 Sa'ad da kuka haye Urdun ɗin sai ku kakkafa waɗannan duwatsu a bisa Dutsen Ebal bisa ga umarnin da na yi muku yau. Ku yi musu shafe da farar ƙasa.
5 Can za ku gina wa Ubangiji Allahnku bagade da duwatsun da ba a taɓa sassaƙa su da baƙin ƙarfe ba.
6 Sai ku gina wa Ubangiji Allahnku bagade da duwatsun da ba a sassaƙa ba. A bisa wannan bagade za ku miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji Allahnku.