3 “Za ku zama masu albarka, ko kuna cikin gari, ko kuna cikin karkara.
4 “'Ya'yanku za su zama masu albarka, haka nan kuma amfanin gonakinku, da 'ya'yan dabbobinku, da 'ya'yan shanunku, da 'ya'yan tumakinku da awakinku.
5 “Kwandunanku da makwaɓan za su yalwata ƙullunku.
6 “Da albarka za ku shiga, da albarka kuma za ku fita.
7 “Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gābanku a gabanku waɗanda suke tasar muku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku.
8 “Ubangiji zai sa wa abin da yake cikin rumbunanku albarka da dukan aikin hannuwanku. Zai sa muku albarka a ƙasar da yake ba ku.
9 “Ubangiji zai sa ku zama tsattsarkar jama'arsa kamar yadda ya rantse muku, idan za ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa.