11 Kamar gaggafar da take kaɗa fikafikanta a kan sheƙarta,Tana rufe da 'yan tsakinta,Ta buɗe fikafikanta, ta kama su,Ta ɗauke su a bisa kafaɗunta.
12 Ubangiji ne kaɗai ya bishe shi,Ba wani baƙon allah tare da shi.
13 “Ya sa shi ya hau kan tuddai,Ya ci amfanin ƙasa,Ya sa shi ya sha zuma daga dutse,Ya ba shi mai daga dutsen ƙanƙara.
14 Ya sami kindirmo daga shanu,Da madara daga garken tumaki da na awaki,Da kitse daga 'yan raguna, da raguna,Da bijimai, da bunsurai daga Bashan,Da alkama mafi kyau.Ka sha ruwan inabi jaja wur, mai kyau.
15 “Yeshurun ya yi ƙiba, yana harbin iska,Ka yi ƙiba, ka yi kauri, ka yi sumul.Ya rabu da Allahn da ya yi shi,Ya raina Dutsen Cetonsa.
16 Suka sa shi kishi, saboda gumaka,Suka tsokani fushinsa da abubuwan banƙyama.
17 Suka miƙa hadayu ga aljannun da ba Allah ba,Ga gumakan da ba su sani ba,Sababbin allolin da aka shigo da su daga baya,Waɗanda kakanninku ba su ji tsoronsu ba.