18 Kun ƙi kula da Dutsen da ya haife ku,Kun manta da Allahn da ya ba ku rai.
19 “Ubangiji ya gani, ya raina su,Saboda tsokanar da 'ya'yansa mata da maza suka yi masa.
20 Ya ce, ‘Zan ɓoye musu fuskata,Zan ga yadda ƙarshensu zai zama.Gama su muguwar tsara ce,'Ya'ya ne marasa aminci.
21 Suka sa ni kishi da abin da ba Allah ba,Suka tsokani fushina da gumakansu,Ni kuma zan sa su su yi kishi da waɗanda suke ba mutane ba.Zan tsokane su da wawanyar al'umma.
22 Gama fushina ya kama wuta,Tana ci har ƙurewar zurfin lahira.Za ta cinye duniya da dukan amfaninta,Za ta kama tussan duwatsu.
23 “ ‘Zan tula musu masifu,Zan ƙare kibauna a kansu,
24 Za su lalace saboda yunwa,Zazzaɓi mai zafi, da muguwar annoba za su cinye su.Zan aika da haƙoran namomi a kansu,Da dafin abubuwa masu jan ciki.