2 Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama,Maganata ta faɗo kamar raɓa,Kamar yayyafi a bisa ɗanyar ciyawa,Kamar ɗiɗɗigar ruwa a bisa ganyaye.
3 Gama zan yi shelar sunan Ubangiji,In yabi girman Allahnmu!
4 “Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne,Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne.Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi,Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
5 Sun aikata mugunta a gabansa,Su ba 'ya'yansa ba ne saboda lalacewarsu,Su muguwar tsara ce, karkatacciya,
6 Haka za ku sāka wa Ubangiji,Ya ku wawaye, mutane marasa hikima?Ba shi ne Ubanku, Mahaliccinku ba,Wanda ya yi ku, ya kuma kafa ku?
7 “Ku fa tuna da kwanakin dā,Ku yi tunani a kan shekarun tsararraki,Ku tambayi mahaifanku, su za su faɗa muku,Ku tambayi dattawanku, su kuma za su faɗa muku,
8 Sa'ad da Maɗaukaki ya ba al'ummai gādonsu,Sa'ad da ya raba 'yan adam,Ya yanka wa mutane wurin zama bisa ga yawan Isra'ilawa.