35 Sakayya da ɗaukar fansa nawa ne,A lokacin ƙafarsu za ta zame,Gama ranar masifarsu ta kusa,Hallakarsu za ta zo da sauri.’
36 Ubangiji zai ɗauka wa jama'arsa fansa,Zai ji ƙan bayinsa,Sa'ad da ya ga ƙarfinsu ya kāsa,Ba kuma wanda ya ragu, bawa ko ɗa.
37 Sa'an nan zai ce, ‘Ina gumakansu,Dutse wanda suka nemi mafaka gare shi,
38 Waɗanda suka ci kitsen hadayunsu,Suka sha ruwan inabin hadayarsu ta sha?Bari su tashi su taimake ku,Bari su zama mafaka!
39 “ ‘Ku duba fa, ni ne shi,Ba wani Allah, banda ni,Nakan kashe, in rayar,Nakan sa rauni, nakan kuma warkar,Ba wanda zai cece su daga hannuna.
40 Na ɗaga hannuna sama,Na rantse da madawwamin raina,
41 Sa'ad da na wasa takobina mai walƙiya,Na riƙe shi da hannuna don yin hukunci,Zan ɗauki fansa a kan magabtanaZan sāka wa maƙiyana.