4 “Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne,Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne.Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi,Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
5 Sun aikata mugunta a gabansa,Su ba 'ya'yansa ba ne saboda lalacewarsu,Su muguwar tsara ce, karkatacciya,
6 Haka za ku sāka wa Ubangiji,Ya ku wawaye, mutane marasa hikima?Ba shi ne Ubanku, Mahaliccinku ba,Wanda ya yi ku, ya kuma kafa ku?
7 “Ku fa tuna da kwanakin dā,Ku yi tunani a kan shekarun tsararraki,Ku tambayi mahaifanku, su za su faɗa muku,Ku tambayi dattawanku, su kuma za su faɗa muku,
8 Sa'ad da Maɗaukaki ya ba al'ummai gādonsu,Sa'ad da ya raba 'yan adam,Ya yanka wa mutane wurin zama bisa ga yawan Isra'ilawa.
9 Gama rabon Ubangiji shi ne jama'arsa,Yakubu shi ne rabon gādonsa.
10 “Ya same shi daga cikin hamada,A jeji marar amfani, inda namomi suke kuka.Ya kewaye shi, ya lura da shi,Ya kiyaye shi kamar ƙwayar idonsa.