18 A kan Zabaluna ya ce,“Ka yi murna da tafiye-tafiyenka, ya Zabaluna,Kai kuma Issaka, cikin alfarwanka.
19 Za su kira mutane zuwa dutse,Can za su miƙa hadayu masu dacewa,Gama za su ɗebo wadatar tekuna,Da ɓoyayyun dukiyar yashi.”
20 A kan Gad, ya ce,“Mai albarka ne wanda ya fāɗaɗa Gad,Gad yana sanɗa kamar zaki,Yana yayyage hannu da ƙoƙon kai.
21 Zai zaɓar wa kansa wuri mai kyau,Gama wurin ne aka keɓe wa shugaba.Ya zo wurin shugabannin mutane,Tare da Isra'ila, ya aikata adalcin Ubangiji,Ya kiyaye farillansa.”
22 A kan Dan, ya ce,“Dan ɗan zaki ne,Mai tsalle daga Bashan.”
23 A kan Naftali, ya ce,“Ya Naftali, ƙosasshe kake da alheri,Cike kake da albarkar Ubangiji.Sai ka mallaki tafki da wajen kudu.”
24 A kan Ashiru, ya ce,“Ashiru mai albarka ne fiye da sauran 'yan'uwansa,Bari ya zama abin ƙauna ga 'yan'uwansa,Ya kuma tsoma ƙafarsa cikin mai.