3 Hakika, yana ƙaunar jama'arsa,Dukan tsarkaka suna a ikonka,Suna biye da kai,Suna karɓar umarninka.
4 Musa ya ba mu dokoki,Abin gādo ga taron jama'ar Yakubu.
5 Ubangiji shi ne sarki a Yeshurun,Sa'ad da shugabanni suka taru,Dukan kabilan Isra'ila suka taru.
6 “Allah ya sa Ra'ubainu ya rayu, kada ya mutu,Kada mutanensa su zama kaɗan.”
7 A kan Yahuza ya ce,“Ka ji muryar Yahuza, ya Ubangiji,Ka kawo shi wurin jama'arsa.Ka yi yaƙi da ikonka dominsu,Ka taimake shi a kan maƙiyansa.”
8 A kan Lawi ya ce,“Ka ba Mai Tsarki Tumminka da Urim naka,Shi wanda ka jarraba a Masaha,Wanda ka yi jayayya da shi a ruwan Meriba,
9 Wanda ya ce wa mahaifinsa da mahaifiyarsa,‘Ban kula da ku ba.’Ya ce wa 'yan'uwansa su ba nasa ba ne.Ya kuma ƙyale 'ya'yansa,Domin sun kiyaye maganarka,Sun riƙe alkawarinka.