7 Musa ya yi shekara ɗari da ashirin sa'ad da ya rasu. Idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuma bai ragu ba.
8 Isra'ilawa suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab har kwana talatin. Sa'an nan kwanakin kuka da makoki domin Musa suka ƙare.
9 Joshuwa ɗan Nun yana cike da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya masa hannuwansa. Isra'ilawa suka yi masa biyayya, suka aikata bisa ga yadda Ubangiji ya umarci Musa.
10 Tun daga lokacin nan, ba a taɓa yin wani annabi a Isra'ila kamar Musa ba, wanda Ubangiji ya san shi fuska da fuska.
11 Ubangiji ya aike shi ya aikata alamu da mu'ujizai a ƙasar Masar a gaban Fir'auna da dukan barorinsa, da dukan ƙasarsa.
12 Ya kuma aikata ayyuka masu iko, masu bantsoro a gaban dukan Isra'ilawa.