1 “Yanzu, ya Isra'ilawa, sai ku kiyaye dokoki da farillai da nake koya muku don ku rayu, ku shiga ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku suke ba ku.
2 Kada ku ƙara, ko ku rage kome daga cikin abin da na umarce ku, amma ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, waɗanda nake umartarku da su.
3 Idanunku sun ga abin da Ubangiji ya yi a Ba'al-feyor, yadda Ubangiji Allahnku ya hallaka dukan mutane daga cikinku da suka bauta wa Ba'al-feyor.
4 Amma ku da kuka dogara ga Ubangiji Allahnku, a raye kuke har yau.