29 Amma idan kun nemi Ubangiji Allahnku a can inda kuke, za ku same shi muddin kun neme shi da zuciya ɗaya, da dukan ranku.
30 Sa'ad da wahala ta same ku, waɗannan abubuwa kuma suka auko muku nan gaba, za ku juyo wurin Ubangiji Allahnku, ku yi masa biyayya.
31 Ubangiji Allahnku, Allah mai jinƙai ne. Faufau, ba zai kunyata ku ba, ba kuwa zai hallaka ku ba, ba kuma zai manta da alkawarin da ya rantse wa kakanninku ba.
32 “Ku tambaya mana, ko a kwanakin dā kafin zamaninku, tun ma daga lokacin da Allah ya yi mutum a duniya, ku tantambaya daga wannan kusurwa ta samaniya zuwa waccan, ko wani babban abu irin wannan ya taɓa faruwa, ko kuma an taɓa jin labarin irinsa?
33 Akwai wata jama'a da ta taɓa jin muryar wani allah tana magana ta tsakiyar wuta kamar yadda kuka ji, har suka rayu?
34 Ko kuma, da akwai wani allah wanda ya taɓa ƙoƙarin fitar da al'umma saboda kansa daga cikin tsakiyar wata al'umma ta wurin wahalai, da alamu, da mu'ujizai, da yaƙi, da nuna iko, da babbar razana kamar yadda Ubangiji Allahnku ya yi dominku a ƙasar Masar a kan idonku duka?
35 An nuna muku wannan don ku sani Ubangiji shi ne Allah, banda shi, ba wani kuma.