2 Ubangiji Allahnmu ya yi alkawari da mu a Horeb.
3 Ba da kakanninmu ne Ubangiji ya yi wannan alkawari ba, amma da mu ne, mu duka waɗanda suke da rai a yau.
4 Ubangiji ya yi muku magana fuska da fuska bisa dutsen ta tsakiyar wuta.
5 Ni ne na tsaya a tsakanin Ubangiji da ku a lokacin don in faɗa muku maganar Ubangiji, gama kun ji tsoro saboda wutar, ba ku kuma hau dutsen ba.“Ubangiji ya ce,
6 ‘Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar daga gidan bauta.
7 “ ‘Kada ka kasance da waɗansu gumaka, sai ni.
8 “ ‘Kada ka yi wa kanka gunki, ko wata siffar abin da yake a sama a bisa, ko siffar abin da yake a duniya a ƙasa, ko siffar abin da yake a cikin ruwa a ƙarƙashin ƙasa.