1 Urushalima wadda take cike da mutane a dā,Yanzu tana zaman kaɗaici!Tana zama kamar mace wadda mijinta ya rasu,Ita wadda dā ta zama babba a cikin sauran al'ummai!Ita wadda take a dā sarauniya a cikin larduna,Ta zama mai biyan gandu!
2 Da dare tana kuka mai zafi,Hawaye suna zuba sharaf-sharaf a kumatunta.Dukan masoyanta ba wanda yake ta'azantar da ita.Dukan abokanta sun ci amanarta, sun zama maƙiyanta.
3 Yahuza ta tafi bauta tana shan azaba,Da bauta mai tsanani.Tana zaune a tsakiyar sauran al'umma,Amma ba ta sami hutawa ba,Gama masu runtumarta sun ci mata, ba hanyar tsira.
4 Hanyoyin Sihiyona suna baƙin cikiDomin ba mai halartar ƙayyadaddun idodi.Dukan ƙofofinta sun zama kufai,Firistocinta suna nishi,Budurwanta kuma suna wahala,Ita kanta ma tana shan wuya ƙwarai.
5 Maƙiyanta sun zama shugabanninta,Abokan gābanta kuma sun zama iyayengijinta.Gama Ubangiji ne ya sa ta sha wahalaSaboda yawan zunubanta.'Ya'yanta sun tafi bauta wurin maƙiyanta.
6 Dukan darajar Sihiyona ta rabu da ita,Shugabanninta sun zama kamar bareyinDa ba su sami wurin kiwo ba,Suna gudu ba ƙarfi a gaban wanda yake korarsu.
7 A kwanakin wahalarta na rashin wurin zama,Urushalima ta tuna da dukan abubuwanta masu daraja a dā.A lokacin da mutanenta suka fāɗa a hannun maƙiyi,Ba wanda ya taimake ta,Maƙiyanta sun gan ta,Sun yi mata ba'a saboda fāɗuwarta.