3 Sun himmantu su aikata abin da yakemugu da hannuwansu.Sarki da alƙali suna nema a ba suhanci,Babban mutum kuma yana faɗar sonzuciyarsa,Da haka sukan karkatar da zance.
4 Mutumin kirkinsu kamar ƙaya yake,Mai gaskiyarsu kuwa kamar shingenƙaya yake.Ranar da kuka sa mai tsaro,A ran nan za a aukar muku dahukunci.Yanzu ruɗewarku ta zo,
5 Kada ka dogara ga maƙwabcinka,Kada kuma ka amince da abokinka.Ka kuma kame bakinka dagamatarkaWadda take kwance tare da kai.
6 Gama ɗa yana raina mahaifi,'Ya kuma tana tayar wamahaifiyarta,Matar ɗa kuma tana gāba dasurukarta,Mutanen gidan mutum su nemaƙiyansa.
7 Amma ni zan kafa ido ga Ubangiji,Zan jira ceton Allahna,Allahna zai ji ni.
8 Ya maƙiyina, kada ka yi murna akaina,Gama sa'ad da na fāɗi, zan tashikuma.Sa'ad da na zauna cikin duhu,Ubangiji zai haskaka ni.
9 Zan ɗauka fushin Ubangiji ne,Gama na yi masa zunubi,Sai lokacin da ya ji da'awata,Har ya yanke mini shari'a.Zai kawo ni zuwa wurin haske,Zan kuwa ga cetonsa.