6 Dukan mutanen Feresa da suka zauna Urushalima su ɗari huɗu da sittin da takwas ne, dukansu kuwa muhimman mutane ne.
7 Waɗannan su ne mutanen Biliyaminu, Sallai ɗan Meshullam, jīkan Yowed. Sauran kakanninsa su ne Fedaiya, da Kolaiya, da Ma'aseya, da Itiyel da Yeshaya.
8 Sa'an nan kuma ga Gabbai da Sallai danginsa, mutum ɗari tara da ashirin da takwas.
9 Yowel ɗan Zikri shi ne shugabansu, Yahuza ɗan Hassenuwa shi ne shugaba na biyu cikin birnin.
10 Na wajen firistoci, su ne Yedaiya ɗan Yoyarib, da Yakin,
11 da Seraiya ɗan Hilkiya, jīkan Shallum. Sauran kakanninsa, su ne Zadok, da Merayot, da Ahitub, mai lura da Haikalin Allah.
12 Tare da 'yan'uwansu waɗanda suka yi aiki a Haikali, su ɗari takwas da ashirin da biyu ne.Akwai kuma Adaya ɗan Yeroham, jīkan Felaliya. Sauran kakanninsa su ne Amzi, da Zakariya, da Fashur, da Malkiya.