22 A zamanin Eliyashib, da Yoyada, da Yohenan, da Yadduwa, Lawiyawa, har zuwa zamanin mulkin Dariyus, mutumin Farisa, aka rubuta shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa da firistoci.
23 Aka kuma rubuta shugabannin gidajen kakannin zuriyar Lawi a tarihi, har zuwa zamanin Yohenan ɗan Eliyashib.
24 Shugabannin Lawiyawa kuwa, su ne Hashabiya, da Sherebiya, da Yeshuwa, da Kadmiyel. 'Yan'uwansu suna tsaye kusa da su daki daki domin su yi yabo, su yi godiya kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.
25 Mattaniya, da Bakbukiya, da Obadiya, da Meshullam, da Talmon, da Akkub su ne masu tsaron ƙofofi, suna tsaron ɗakunan ajiya na wajen ƙofofi.
26 Waɗannan suna nan a zamanin Yoyakim ɗan Yeshuwa, jikan Yehozadak, da zamanin mai mulki Nehemiya, da Ezra, firist da magatakarda.
27 A lokacin keɓe garun Urushalima, sai aka nemo Lawiyawa a wurarensu duka don a kawo su Urushalima, su yi bikin keɓewa da farin ciki da godiya, da raira waƙoƙi da kuge, da garaya, da molo.
28 Aka tattara mawaƙa daga kewayen Urushalima da ƙauyukan Netofatiyawa.