28 Aka tattara mawaƙa daga kewayen Urushalima da ƙauyukan Netofatiyawa.
29 Da kuma daga Betgilgal da karkarar Geba, da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.
30 Sai firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma tsarkake jama'a, da ƙofofi, da garun.
31 Sai na sa shugabannin Yahuza su hawo garu, sa'an nan na sa manyan ƙungiyoyi biyu waɗanda za su yi godiya, su tafi a jere.Ƙungiya guda ta bi wajen dama a kan garun zuwa Ƙofar Juji.
32 Hoshaiya da rabin sugabannin Yahuza suka bi bayansu,
33 tare da Azariya, da Ezra, da Meshullam,
34 da Yahuza, da Biliyaminu, da Shemaiya, da Irmiya.