17 Sa'an nan na ce musu, “Kun ga irin wahalar da muke ciki, yadda Urushalima ta zama kango, an kuma ƙone ƙofofinta. Ku zo, mu sāke gina garun Urushalima don mu fita kunya.”
18 Na kuma faɗa musu yadda Allah yana tare da ni, ya kuma taimake ni, da maganar da sarki ya faɗa mini.Sai suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Suka himmatu su yi wannan aiki nagari.
19 Amma sa'ad da Sanballat Bahorone, da Tobiya Ba'ammone, bawa, da Geshem Balarabe, suka ji labari, sai suka yi mana ba'a, suka raina mu, suka ce, “Me kuke yi? Kuna yi wa sarki tayarwa ne?”
20 Ni kuwa sai na amsa musu, na ce, “Allah na Sama zai ba mu nasara, saboda haka mu mutanensa za mu tashe, mu kama gini, amma ba ruwanku, ba hakkinku, ba ku da wani abin tunawa a Urushalima.”