1 Sa'ad da Sanballat ya ji muna ginin garun, sai ya husata ƙwarai, ya yi wa Yahudawa ba'a.
2 Ya yi magana a gaban 'yan'uwansa da sojojin Samariya ya ce, “Mene ne waɗannan Yahudawa kumamai suke yi? Za su mai da abubuwa yadda suka a dā ne? Za su miƙa hadayu ne? Za su gama ginin a rana ɗaya ne? Za su iya samun duwatsun gini daga tsibin matattun duwatsu?”
3 Tobiya Ba'ammone yana kusa da shi, ya ce, “Ai, garun da suke ginawa da duwatsu, ko dila ya hau, sai ya rushe shi!”
4 Sai ni, Nehemiya, na yi addu'a, na ce, “Ka ji, ya Allahnmu, gama ana raina mu, ka sa ba'arsu ta koma kansu, ka sa a washe su a kai su ƙasar bauta.
5 Kada ka shafe laifinsu, kada kuwa ka gafarta musu, gama sun ci mutuncinmu, mu da muke gini.”
6 Muka gina garun, har ya kai rabin tsayinta, domin mutane sun himmatu da aikin.