5 Kada ka shafe laifinsu, kada kuwa ka gafarta musu, gama sun ci mutuncinmu, mu da muke gini.”
6 Muka gina garun, har ya kai rabin tsayinta, domin mutane sun himmatu da aikin.
7 Amma sa'ad da Sanballat, da Tobiya, da Larabawa, da Ammonawa, da mutanen Ashdod, suka ji yadda ginin garun Urushalima yake ci gaba, ana kuma tattoshe tsattsaguwa, sai suka husata.
8 Dukansu suka ƙulla za su zo, su yi yaƙi da Urushalima, su ta da hankali a cikinta.
9 Sai muka yi addu'a ga Allahnmu, muka sa masu tsaro su yi mana tsaro dare da rana saboda su.
10 Mutanen Yahuza kuwa suka ce,“Ƙarfin ma'aikata yana kāsawa,Akwai komatsai da yawa da za a kwashe,Yaya za mu iya gina garun yau?”
11 Abokan gābanmu kuma suka ce, “Ba za su sani ba, ba kuwa za su gan mu ba, sai dai kawai su gan mu a cikinsu, za mu karkashe su, mu tsai da aikin.”