1 Sai mata da maza suka yi ta kuka ƙwarai saboda 'yan'uwansu Yahudawa.
2 Akwai waɗanda suka ce, “Mu da 'ya'yanmu mata da maza muna da yawa, sai mu sami hatsi don mu ci mu rayu.”
3 Waɗansu kuma suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.”
4 Akwai waɗansu kuma da suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu.