16 Na mai da hankali ga aikin garu, ban samar wa kaina gonaki ba. Barorina duka suka haɗa kai da ni a kan aikin gini.
17 Duk da haka akwai Yahudawa da shugabanni ɗari da hamsin waɗanda suke cin abinci a teburina, banda waɗanda sukan zo wurinmu daga al'umman da suke kewaye da mu.
18 Ga abincin da ake shiryawa kowace rana, sa ɗaya, da tumaki shida kyawawa, da kuma kaji. A kowace rana ta goma akan kawo salkunan ruwan inabi masu yawa, amma duk da haka ban karɓi albashin da akan ba mai mulki ba, domin wahala ta yi wa mutane yawa.
19 Ya Allahna, ka tuna da alherin da na yi wa mutanen nan.