16 Sa'ad da abokan gābanmu da dukan al'umman da suke kewaye da mu suka ji, sai suka ji tsoro, gabansu kuma ya faɗi, gama sun gane, da taimakon Allahnmu muka yi wannan aiki.
17 A kwanakin nan kuma shugabannin Yahuza suka yi ta aika wa Tobiya da wasiƙu, shi kuma Tobiya yana ta aika musu da nasa wasiƙu.
18 Mutane da yawa a Yahuza sun rantse za su goyi bayan Tobiya, domin ya auri 'yar Shekaniya, ɗan Ara. Ɗansa kuma, wato Yohenan, ya auri 'yar Meshullam, ɗan Berikiya.
19 Mutane suka yi magana a kan ayyukan kirki na Tobiya a gabana. Suka kuma kai maganata a wurinsa, sai Tobiya ya yi ta aika mini da wasiƙu don ya tsoratar da ni.