Neh 7:26-38-57-59 HAU

26-38 Mutanen da kakanninsu suka zauna a waɗannan garuruwa, su ma sun komo daga zaman talala.Baitalami da Netofa, ɗari da tamanin da takwasAnatot, ɗari da ashirin da takwasAzmawet, arba'in da biyuKiriyat-yeyarim da Kefira, da Biyerot, ɗari bakwai da arba'in da ukuRama da Geba, ɗari shida da ashirin da ɗayaMikmash, ɗari da ashirin da biyuBetel da Ai, ɗari da ashirin da ukuDa wani Nebo, hamsin da biyuDa wani Elam, dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)Harim, ɗari uku da ashirinYariko, ɗari uku da arba'in da biyarLod, da Hadid, da Ono, ɗari bakwai da ashirin da ɗayaSenaya, dubu uku da ɗari tara da talatin (3,930)

39-42 Ga lissafin iyalin firistoci da suka komo daga zaman talala.Yedaiya, na zuriyar Yeshuwa, ɗari tara da saba'in da ukuImmer, dubu ɗaya da hamsin da biyu (1,052)Fashur, dubu da ɗari biyu da arba'in da bakwai (1,247)Harim, dubu ɗaya da goma sha bakwai (1,017)

43 Lawiyawan da suka komo daga zaman talala, Yeshuwa da Kadmiyel na zuriyar Hodawiya, saba'in da huɗu.

44 Mawaƙa, na zuriyar Asaf, ɗari da arba'in da takwas.

45 Masu tsaron Haikali su ne zuriyar Shallum, da Ater, da Talmon, da Akkub, da Hatita, da Shobai, ɗari da talatin da takwas.

46-56 Ma'aikatan Haikali da suka komo daga zaman talala, su neZuriyar Ziha, da Hasufa, da Tabbawot,Keros, da Siyaha, da Fadon,Lebana, da Hagaba, da Shamlai,Hanan, da Giddel, da Gahar,Rewaiya, da Rezin, da Nekoda,Gazam, da Uzza, da Faseya,Besai, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa,Bakbuk, da Hakufa, da Harkur,Bazlut, da Mehida, da Harsha,Barkos, da Sisera, da Tema,Neziya, da Hatifa.

57-59 Iyalan barorin Sulemanu da suka komo daga zaman talala, su nena Sotai, da Hassoferet, da Feruda,Yawala, da Darkon, da Giddel,Shefatiya, da Hattil, da Fokeret-hazzebayim, da Ami.