39-42 Ga lissafin iyalin firistoci da suka komo daga zaman talala.Yedaiya, na zuriyar Yeshuwa, ɗari tara da saba'in da ukuImmer, dubu ɗaya da hamsin da biyu (1,052)Fashur, dubu da ɗari biyu da arba'in da bakwai (1,247)Harim, dubu ɗaya da goma sha bakwai (1,017)
43 Lawiyawan da suka komo daga zaman talala, Yeshuwa da Kadmiyel na zuriyar Hodawiya, saba'in da huɗu.
44 Mawaƙa, na zuriyar Asaf, ɗari da arba'in da takwas.
45 Masu tsaron Haikali su ne zuriyar Shallum, da Ater, da Talmon, da Akkub, da Hatita, da Shobai, ɗari da talatin da takwas.
46-56 Ma'aikatan Haikali da suka komo daga zaman talala, su neZuriyar Ziha, da Hasufa, da Tabbawot,Keros, da Siyaha, da Fadon,Lebana, da Hagaba, da Shamlai,Hanan, da Giddel, da Gahar,Rewaiya, da Rezin, da Nekoda,Gazam, da Uzza, da Faseya,Besai, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa,Bakbuk, da Hakufa, da Harkur,Bazlut, da Mehida, da Harsha,Barkos, da Sisera, da Tema,Neziya, da Hatifa.
57-59 Iyalan barorin Sulemanu da suka komo daga zaman talala, su nena Sotai, da Hassoferet, da Feruda,Yawala, da Darkon, da Giddel,Shefatiya, da Hattil, da Fokeret-hazzebayim, da Ami.
60 Jimillar zuriyar ma'aikatan Haikali da na Sulemanu, su ɗari uku da tasa'in da biyu ne.