43 Lawiyawan da suka komo daga zaman talala, Yeshuwa da Kadmiyel na zuriyar Hodawiya, saba'in da huɗu.
44 Mawaƙa, na zuriyar Asaf, ɗari da arba'in da takwas.
45 Masu tsaron Haikali su ne zuriyar Shallum, da Ater, da Talmon, da Akkub, da Hatita, da Shobai, ɗari da talatin da takwas.
46-56 Ma'aikatan Haikali da suka komo daga zaman talala, su neZuriyar Ziha, da Hasufa, da Tabbawot,Keros, da Siyaha, da Fadon,Lebana, da Hagaba, da Shamlai,Hanan, da Giddel, da Gahar,Rewaiya, da Rezin, da Nekoda,Gazam, da Uzza, da Faseya,Besai, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa,Bakbuk, da Hakufa, da Harkur,Bazlut, da Mehida, da Harsha,Barkos, da Sisera, da Tema,Neziya, da Hatifa.
57-59 Iyalan barorin Sulemanu da suka komo daga zaman talala, su nena Sotai, da Hassoferet, da Feruda,Yawala, da Darkon, da Giddel,Shefatiya, da Hattil, da Fokeret-hazzebayim, da Ami.
60 Jimillar zuriyar ma'aikatan Haikali da na Sulemanu, su ɗari uku da tasa'in da biyu ne.
61-62 Waɗannan su ne daga zuriyar Delaiya, da Tobiya, da Nekoda, waɗanda suka zo daga garuruwan Telmela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya nuna gidajen kakanninsu, ko zuriyarsu a cikin Isra'ilawa ba, su ɗari shida ne da arba'in da biyu.