18 Ko sa'ad da suka yi wa kansu ɗan marakin zubi,Suka ce shi ne allahn da ya fisshe su daga Masar,Ai, sun yi maka ɓatanci, ya Ubangiji.
19 Amma ba ka rabu da su a hamada ba,Saboda jinƙanka mai girma ne.Ba ka kuwa kawar da girgije da wuta ba,Waɗanda suke nuna musu hanya dare da rana.
20 Ta wurin alherinka ka faɗa musu abin da ya kamata su yi,Ka ciyar da su da manna, ka ba su ruwa su sha.
21 Ka taimake su a jeji shekara arba'in,Ka ba su dukan abin da suke bukata,Ƙafafunsu ba su kumbura su yi musu ciwo ba.
22 “Ka sa sun ci al'ummai da mulkoki da yaƙi,Ƙasashen da suke maƙwabtaka da tasu.Suka ci ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon,Da ƙasar Bashan, inda Og yake sarki.
23 Ka riɓaɓɓanya zuriyarsu kamar taurarin sararin sama,Ka sa suka ci ƙasar, suka zauna cikinta,Ƙasar da aka yi wa kakanninsu alkawari za ka ba su.
24 Saboda haka zuriyarsu suka shiga, suka mallaki ƙasar Kan'ana.Ka rinjayi mutanen da suke zama a can.Ka ba jama'arka iko su yi yadda suke soDa mutane, da sarakunan ƙasar Kan'ana.