25 Sun ci birane masu garu, da ƙasa mai dausayi,Da gidaje cike da dukiya, da rijiyoyi, da gonakin inabi,Da itatuwan zaitun, da itatuwa masu 'ya'ya.Suka ci dukan abin da suke so, suka yi taiɓa,Suka mori dukan kyawawan abubuwan da ka ba su.
26 “Amma suka yi maka rashin biyayya, suka tayar maka,Suka juya wa dokokinka baya,Suka karkashe anna bawan da suka faɗakar da su,Waɗanda suka faɗa musu su juyo gare ka.Suka yi ta saɓa maka lokaci lokaci.
27 Saboda haka ka bar abokan gābansu su ci su, mallake su.A wahalarsu sun yi kira gare ka domin taimako,Ka kuwa amsa musu daga Sama.Ta wurin jinƙanka mai yawa ka aiko musu da shugabanni,Waɗanda suka kuɓutar da su daga maƙiyansu.
28 Sa'ad da zaman salama ya komo, sai kuma su yi zunubi,Kai kuma sai ka bar abokan gabansu su ci su.Duk da haka idan sun tuba, suka roƙe ka ka cece su,Kakan ji daga Sama,sau da yawa,Ka cece su da jinƙanka mai yawa.
29 Ka gargaɗe su su yi biyayya da koyarwarka,Amma sun bijire wa dokoki saboda girmankai,Ko da yake kiyaye dokarka ita ce hanyar rai.Masu taurinkai sun taurare, sun ƙi yin biyayya.
30 “Ka yi haƙuri da su shekaru da yawa, ka gargaɗe su,Annabawanka sun yi musu magana, amma sun toshe kunne.Saboda haka ka sa waɗansu al'ummai su mallaki jama'arka.
31 Duk da haka, saboda yawan jinƙanka,Ba ka yashe su ko ka hallaka su ba.Kai Allah mai alheri ne mai jinƙai!