29 Ka gargaɗe su su yi biyayya da koyarwarka,Amma sun bijire wa dokoki saboda girmankai,Ko da yake kiyaye dokarka ita ce hanyar rai.Masu taurinkai sun taurare, sun ƙi yin biyayya.
30 “Ka yi haƙuri da su shekaru da yawa, ka gargaɗe su,Annabawanka sun yi musu magana, amma sun toshe kunne.Saboda haka ka sa waɗansu al'ummai su mallaki jama'arka.
31 Duk da haka, saboda yawan jinƙanka,Ba ka yashe su ko ka hallaka su ba.Kai Allah mai alheri ne mai jinƙai!
32 “Ya Allah, Allahnmu, da girma kake!Kai mai banrazana ne, cike da iko!Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta.Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu,Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba!Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu,Da annabawanmu, da kakanninmu,Da dukan sauran jama'arka sun sha wahala.Ka san irin wahalar da muka sha.
33 Ka yi daidai da ka hukunta mu haka!Kai mai aminci ne, mu kuwa mun yi zunubi.
34 Gama kakanninmu, da sarakunanmu,Da shugabanninmu, da firistocinmu,Ba su kiyaye dokarka ba.Ba su kasakunne ga umarnanka da gargaɗinka ba.Da waɗannan ne kake zarginsu.
35 Da albarkacinka sarakuna suke mulkin jama'arka,Sa'ad da suke ƙasashen waje, ƙasa mai dausayi ka ba su,Amma ba su juyo su bar zunubi, su bauta maka ba.