1 Na'omi tana da wani dangin mijinta, Elimelek, sunansa Bo'aza, shi kuwa attajiri ne.
2 Sai Rut, mutuniyar Mowab, ta ce wa Na'omi, “Bari in tafi, in yi kalan hatsi a gonar wanda ya yarda in yi.”Na'omi ta ce mata, “Ki tafi, 'yata.”
3 Rut ta tafi wata gona, tana bin bayan masu girbi, tana kala. Ta yi sa'a kuwa ta fāɗa a gonar Bo'aza, dangin Elimelek.
4 Sai ga Bo'aza ya zo daga Baitalami, ya ce wa masu girbi, “Salamu alaikun.”Suka amsa, “Alaika salamu.”
5 Sa'an nan Bo'aza ya tambayi baransa da yake shugaban masu girbin, ya ce, “'Yar wace ce wannan?”