1 Ubangiji kuwa ya yi magana da Yusha'u ɗan Beyeri a zamanin mulkin Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, sarakunan Yahuza, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yehowash, Sarkin Isra'ila.
2 Sa'ad da Ubangiji ya fara yin magana da Yusha'u ya ce masa, “Tafi ka auro karuwa, ka haifi 'ya'yan karuwanci, gama ƙasar tana yin fasikanci sosai, wato ta bar bin Ubangiji.”
3 Sai ya tafi ya auri Gomer, 'yar Diblayim. Ta yi ciki, ta haifi masa ɗa namiji.
4 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Yezreyel, gama ba da daɗewa ba zan ziyarci gidan Yehu da hukunci saboda jinin da ya zubar a Yezreyel. Zan sa mulkin Isra'ila ya ƙare.