8 Sa'ad da ta yaye Ba-jinƙai, ta sāke ɗaukar ciki, ta haifi ɗa namiji.
9 Ubangiji kuma ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Ba-mutanena-ba-ne, gama ku ba mutanena ba ne,ni kuma ba Allahnku ba ne.
10 “Duk da haka yawan mutanen Isra'ilaZai zama kamar yashi a bakin teku,Wanda ba za a iya aunawa ko ƙidayawa ba.Maimakon kuma a ce, ‘Ku ba mutanena ba ne,’Za a ce, ‘Ku mutanen Allah ne mai rai.’
11 Mutanen Yahuza da mutanen Isra'ila za su haɗu su zama ɗaya,Za su zaɓa wa kansu shugaba ɗaya.Za su shugabanci ƙasarGama ranar Yezreyel babba ce.”